Kalli Yadda ‘Yan Najeriya Ke Hawan Gini Don Neman Aikin NDLEA A Jihar Kano

Naija News a yau ta ci karo da wani faifan bidiyo da hotuna mai bacin hali da ban tsoro hadi da cin mutunci da Hukumar Kula da Amfani Da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) suka sanya masu neman shiki hukumar aikin.

Daga faifan bidiyon da aka raba ta yanar gizo, an gano yadda masu neman aiki da yawa suna hawa ginin hukumar don samun shiga dakin gwajin cancantar samun aiki da hukumar tarayya ta shirya wa ma’aikatan.

Wannan kamfanin dilancin labarai ta fahimci cewa masu neman aikin sunyi hakan ne don yanayin da aka sanya su na tsayi cikin rana da tsawon awannai a yayin da suke jiran shiga jarabawan.

Kalli Bidiyo da Hotuna a kasa;