Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 19 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 19 ga Watan Disamba, 2019

1. An Tsige Shugaba Donald Trump

Majalisar Wakilan Amurka ta gurfanar da Shugaban Amurka Donald Trump saboda cin zarafin iko da toshewar Majalisa.

Naija News ta ba da rahoton cewa, Majalisar Wakilai ta tsige Trump a daidai karfe 8:23 na yamma a ranar Laraba bayan wata muhawara mai zafi da jefa kuri’un kan wasu zance biyu da aka wallafa na tsige shi bayan makonni na shaidar alaka da huldarsa da Ukraine.

2. Kalli Yadda TB Joshua Ta Bayyana Rikicin Tsigewar Donald Trump

Wani faifan bidiyo da aka gano a kan yanar gizo ya bayyana yadda wani Annabin Najeriya da kuma babban Fasto na Ikilisiyar Synagogue of All Nations, TB Joshua ta annabta ‘kuri’ar rashin amincewa’ kan Shugaban Amurka, Donald Trump.

A ranar 6 ga Nuwamba 2016, ‘yan kwanaki kafin zaben Amurka wanda Shugaba Donald Trump ya yi nasara, TB Joshua ya yi hasashen cewa wanda ya lashe zaben Amurka zai fuskanci kalubale, gami da’ kuri’ar rashin amincewa.

3. Cikakken Jerin Gwamnonin Da Kotun Koli Ta yi hukunci a kan zabinsu

Kotun kolin Najeriya a ranar Laraba ta bayar da hukuncin karshe na zaben gwamnoni takwas a zaben gwamnoni na 2019.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa kotun Apex ta amince da zaben dukkan gwamnoni takwas din.

4. APC Tayi Rashi A Yayin Da Wani Sanata Ya Mutu A Jihar Imo

Sanata Benjamin Uwajumogu, Sanata mai wakiltar mazabar Arewacin Imo a majalisar dattijan Najeriya ya rasu.

Naija News ta rahoto cewa Sanata Uwajumogu ya fadi ne cikin makewayin gidansa a yayin da yake wanka, an garzaya da shi wani asibiti mai zaman kanta a Apo, cikin Abuja, babban birnin Najeriya, inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

5. Shugaba Buhari Ya Shirya Gyara Tsarin Kasafin Shekarar 2020 (Duba Dalili)

Wannan shawarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na neman gyara ga kasafin kudin shekarar 2020 ta hanyar aika da shawarwari ga Majalisar Dokoki ta kasa za a iya kamanta shi da kwaskwariman kasafin kudi ga majalisa.

Naija News ta fahimci cewa Shugaban kasar, wanda ya sanya hannu kan kasafin kudin N10.59 trillion a ranar Talata, ya gano cewa akwai wasu kari ga kasafin shekarar 2020 kamar yadda ‘yan majalisar suka gabatar.

6. Shugaba Buhari Ya Nada Sabbin Sakatarorin Dindindin – Kalli Sunayansu

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsar da matar Ministan kwadago da aiki, Dr (Misis) Evelyn Ngige da wasu mutane takwas a matsayin sabbin Sakatarorin Dindindin a ranar Laraba.

Wannan sanarwar ya fito ne daga hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan farar hula na tarayya (Ag. HoCSF), Dr. Folashade Yemi-Esan.

7. Shugaba Buhari Yayi Sabon Nadi Shugaban DPR

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sarki Auwalu a matsayin Daraktan Sashen Kula da albarkatun Man Fetur (DPR).

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Auwalu zai shugabanci sashen a wa’adi na farko na shekaru hudu.

8. Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Sanar Da Shirinta Na Gina Masallacin Juma’a 90

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da shirinta na gina masallacin Juma’a 90 inda al’umma zasu rika yin salla biyar na kowace rana.

Hakan ya bayyana ne daga bakin kakakin ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Isma’il Ibrahim, wanda ya tabbatar da wannan ci gaba kuma ya kara bayyana cewa sama da ‘yan kwangila 200 ne suke neman a yardar masu da yin aikin gina masallatan wadda za a gina a gundumomi 30 na jihar.

Ka Samu kari da Cikakken Labaran Najeriya Na Yau A Shafin Naija News Hausa