Connect with us

Uncategorized

Sakon Atiku Ga Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki Na Murnan Shekaru 57 Ga Haifuwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki murnar cika shekara 57 da haihuwa.

Atiku wanda ya yi amfani da shafinsa na Twitter domin tayin murna ga tsohon gwamnan jihar Kwara din ya yi addu’ar Allah ya ba shi karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya.

Sakon sa na kamar haka;

“A madadin iyalina, ina taya @bukolasaraki murna da farin cikin ranar haihuwa. Allah Ya ba ka shekaru masu yawa cikin koshin lafiya da ci gaba da hidimtawa Najeriya.”

Haka kuwa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yaba wa Saraki saboda irin gagarumar gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya lokacin da yake matsayin Shugaban Majalisar Dattawa a Majalisar Wakilai ta 8.

Gwamnan a cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun sa, Olisa Ifeajika, ya bayyana cewa rawar gani da Saraki ya taka a matsayin Babban Darekta a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a babban zaben 2019 ya yi matukar shahara duk da cewa jam’iyyar ta sha kaye a zaben shugaban kasa.

Ka tuna da cewa Bukola Saraki shi ne shugban Majalisar Dattawar Najeriya a Majalisa na 9, kafin ya sha kaye a babban zaben 2019 da ya gudana a watan Fabrairu.