Connect with us

Uncategorized

‘Yan bindiga Sun Sace Wani Farfesa Na Jami’ar MAUTECH A Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘yan bindiga da ake zato da zaman ‘yan fashi sun sace wani farfesa na sashen Fishery na Jami’ar Fasaha ta Moddibo Adama (MAUTECH), Yola, Kayode Shogbesan, bisa bayanin ‘yan sanda da mazauna.

Naija News Hausa tattara da cewa wannan shine karo na uku cikin watanni ukun da aka sace malamin jami’ar.

Wata majiyar daga iyalin da abin ya shafa ta fada a ranar Laraba cewa, an sace Kayode Shogbesan, wanda shi ma, fasto ne a cocin Redeemed Christian Church of God, Yola, a ranar Talata da daddare.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce an sace malamin ne yayin da yake dawowa gida daga ofis tsakanin karfe 8 na dare zuwa 9 a ranar Talata.

A safiyar ranar Talata, 17 ga Disamba, an sace wasu mutane guda biyar ‘yan gida guda a shiyar Ganye, hedkwatar karamar hukumar Ganye.

Idan za a iya tunawa, Farfesa Felix Ilesanmi na Sashen Urban da Regional Planning a jami’ar, shima an sace shi a watan da ya gabata, 15 ga Nuwamba.

Haka kazalika a ranar 30 ga Satumbar, Farfesa Adamu Zata na Shafin Kimiyya kan Kasa shi ma an sace shi.

Kamfanin dilancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa hare-haren wacce aka bayyana da wuce gona da iri saboda yawar sace mutane, a yanzu ya zama abin tashin hankali a yayin da mazaunan sun kasa yin bacci tare da rufe idanunsu biyu a jihar.

KARANTA WANNAN KUMA; Mataimakin Gwamna Kebbi Yasa ‘Yan Ta’adda Dukar Wasu Mawaka 8 Don Sukar Gwamna Bagudu