Connect with us

Labaran Najeriya

Donald Trump: ‘Yan Najeriya Sun Nemi A Tsige Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Najeriya sun tafi shafin yanar gizo na Twitter don neman tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ya bayar da rahoton cewa, bukatar da ‘yan Najeriya ya biyo ne bayan da Majalisar Wakilai ta Amurka suka dauki matakin tsige Shugaba Donald Trump na Amurka.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Majalisar Wakilan Amurka ta gurfanar da Shugaban Amurka Donald Trump saboda cin zarafin iko da toshewar Majalisa.

Naija News ta ba da rahoton cewa, Majalisar Wakilai ta tsige Trump a daidai karfe 8:23 na yamma a ranar Laraba bayan wata muhawara mai zafi da jefa kuri’un kan wasu zance biyu da aka wallafa na tsige shi bayan makonni na shaidar alaka da huldarsa da Ukraine.