Connect with us

Uncategorized

Ganduje Ya Baiwa Sarki Sanusi Kwana Biyu Don Daukan Wasu Matakai Ko Ya Tsige Shi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya baiwa mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido, kwana biyu don karba ko kin amincewa da nadin nasa.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano ya nada Sanusi a matsayin Shugaban Majalisar Masarautar Kano.

‘Yan kwanaki bayan nadin da gwamnatin Ganduje ta nada, Mai Martaba Sarkin Kano ya ki sanar da gwamnatin jihar game da yarda ko kin amincewa da nadin.

Gwamna Ganduje a cikin wata sanarwa da aka bayar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana zancen baiwa sarki Sanusi kwana biyu kawai don bayyana ra’ayinsa.

Sakon na kamar haka;

“Gwamnatin jihar Kano ta bayar wa Mai martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido, kwana biyu kacal don sanar da gwamnatin jihar da ra’ayinsa kan amince ko rashin amincewa da matsayin da aka bashi na zaman Shugaban Majalisar Masarautar Kano.”

Ku tuna kamar yadda Naija News Hausa ta sanar a baya, cewa Babbar kotun jihar Kano ta baiwa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ganduje ikon cire duk wani sarki a cikin a bisa tsarin doka.

Mai shari’a A. T. Badamasi wanda ya sanar da haka a Kotu bayan ya ki bayar da damar tsawaita karar umarnin  hana gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar kutsa kai da kuma iko kan masarautar Kano.