Connect with us

Labaran Najeriya

Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Ya Karbi Nadin Da Gwamna Ganduje Yayi Masa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoton da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa Mai martaba Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya ba da sanarwar amince da nadin nasa a matsayin shugaban majalisar masarautar jihar Kano.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya baiwa mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido, kwana biyu don bayyana ra’ayinsa da mukamin da aka bashi ko kuma ya tsige shi daga kujerar sarauta.

A yau 20 ga Disamba 2019, Mataimakin gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi kira da suna Dawisu ya sanar da tabbaci da cewa sarki Sanusi ya amince da nadin da aka yi masa.

Sakon wadda aka wallafa a shafin yanar gizon zumunta na Twitter na kamar haka;

“Mai martabar, Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, a yau, ya amince da nadin nasa da H.E @GovUmarGanduje ya yi a matsayin Shugaban Majalisar Masarautar Kano, wanda ya kunshi dukkan masarautuka 5 a jihar da sauran membobi.”

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Najeriya Ba Za Su Sake Barci Ba Da Sun San Abin Da Ke Gudana a Kasar – TY Danjuma