Connect with us

Uncategorized

Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna Sun Bada Tabbacin Sace Hakimi Da Mutane Hudu da Aka Yi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta bayyana tabbacin sace Alhaji Yahaya Abubakar (Sarkin Kudu), Shugaban Gundumar Birnin Gwari da Alhaji Ibrahim Musa, tsohon sakataren ilimi na karamar hukumar Birnin Gwari da aka yi a ranar 18 ga Disamba a jihar Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Yakubu Sabo ya ba da tabbacin lamarin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

Sabo ya ce rundunar ta samu bayanin wasu munanan alamura guda biyu da suka faru na sace-sacen mutane ta hannun DPOs na Buruku da Sabon Tasha bi da bi.

“A ranar 18 ga Disamba da misalin karfe 2:30, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun fada wa wata mota da hari akan titin Birnin Gwari ta hanyar unguwan Yako inda suka sace mutane biyu zuwa inda ba wanda ya san da ita.” inji Mista Sabo.

Ya bayyana wadanda abin ya shafa sun hada da Alhaji Yahaya Abubakar (Sarkin Kudu), shugaban gundumar Birnin Gwari da Alhaji Ibrahim Musa, tsohon sakataren ilimi na karamar Birnin Gwari.

Ya kuma bayar da cewa, wannan mummunan abin da ya faru na sace mutanen an yi shi ne a Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun, inda mutane uku wato; Jonathan Obi, Joakin Obi da Benjamin Obi dukkansu ‘yan shiya guda a misalin karfe biyu na tsakar ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba ta hannun wasu mahara da bindiga.

“Bayan karbar wannan bayanin, anan take muka watsar da rukunin ‘yan Sanda da ke yaki da satar mutane, SARS da IRT zuwa bangarorin biyu.”

Sabo ya kara da cewa rundunar ta yi matukar bakin ciki da wannan lamari da ya faru, kuma tana yin dukan kokarinta don gano wadanda suka aikata wannan laifi tare da kubutar da wadanda abin ya shafa.

“Kwamishinan ‘yan sanda, Ali Janga yana kira ga jama’a da kada su bar tsoron wannan al’amari ya dame su a yayin da rundunar ta riga ta kutsa kai ga tabbatar da cewa an kubutar da wadanda abin ya shafa.”