Connect with us

Labaran Najeriya

‘Yan Najeriya Ba Za Su Sake Barci Ba Da Sun San Abin Da Ke Gudana a Kasar – TY Danjuma

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Janar Theophilus Danjuma (rtd), tsohon Ministan Tsaro a Najeriya ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba za su sake yin bacci ba idan ya bayyana abin da ke faruwa a kasar a halin da ake ciki yanzunnan.

Da yake karin bayani, tsohon Janar din mai ritaya ya yi kuka da cewa kowa da kowa sun rasa muryarsu da kuma ya tsorata, musanman a kasar Yarbawa.

Danjuma ya gabatar da hakan ne yayin da yake magana a ranar Alhamis a Ibadan yayin kaddamar da wani littafi na Shekaru 70 na Ci gaban Jarida.

Ya ce: “A ƙasar Yarbawa, da alama kowa ya rasa muryar sa, da kuma tsorace. Kuma da alamun mutane basu damu da abin da ke gudana ba. Idan na fada muku abinda na sani da ke faruwa a kasar Najeriya yau, ba zaku sake yin bacci ba.”

“Muna cikin wani mawuyacin hali. Kuma mutanen da suka saka mu cikin wannan yanazi sun ci gaba a yau da hakan kuma. Don haka, ya kamata mu farka. Mu ne kawai zamu iya ceton kanmu.”

“Rashim jituwa da ke gudana tsakanin jama’arku ba su taimakawa al’amura ko kadan. Allah Ta’ala Ya ci gaba da sanya wa kasar nan albarka, amma dai mu ne kawai zamu iya kubutar da kanmu daga hakan.”

KARANTA WANNAN KUMA; Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai gamsu da tsarin dimokuradiyya ba, musanman yanayin tafiyar hawainiya ta tsarin ba.

[le id=”1″]