Connect with us

Uncategorized

2023: Atiku Na Da ‘Yancin Fita Takara A Zabe Na Gaba – Inji Shugaban BoT

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Shugaban, kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Walid Jibrin, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na da ‘yanci don neman tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Kaduna, jigon a jam’iyyar PDP ya ce duk wani mai so da kuma ke da cancanci a jam’iyyar daga kowane bangare na Najeriya yana da ‘yancin neman tsayawa takarar shugaban kasa a tsarin sa.

Ku tuna a baya da cewa Naija News Hausa ta ruwaito da cewa bayan yawan gwagwarmaya da jaye-jaye, Kotun kara akan hidimar zaben kasa ta bayyana dagewa da kin bada dama ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ga zaben 2019, don binciken na’urar da hukumar INEC tayi amfani da shi wajen hidimar zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

Kotun tayi hakan ne bayan da hukumar INEC ta dage da cewa basu yi amfani da wata na’urar kwamfuta ba wajen ajiye sakamakon zaben 2019.