Connect with us

Labaran Najeriya

Jonathan Ya Shawarci Shugaba Buhari Kan Matakin Da Zai Dauka Ga Maharansa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari da ta kama tare da tsananta wa ‘yan bindigar da suka kai hari gidansa a Otuoke, Jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, tsohon shugaban bai sami rauni ba a harin wanda mutane da yawa ke zargin cewa ana son ne kashe shi.

Wani jami’in tsaro da aka sanya a gidan tsohon shugaban kasar ya mutu a harin amma ‘yan sanda basu fitar da sanarwa ba tukunna.

Da yake jawabi yayin da yake jagorantar masu juyayi a wurin da aka kai harin ranar Juma’a, Jonathan ya godewa ‘yan Najeriya kan nuna hadin kai da juyayi bayan harin da aka yi wa gidansa a ranar Kirsimeti.

Ya kuma yaba wa rundunar sojojin Najeriya saboda yunkuri da suka yi na gamewa da munsayar wuta da maharan a cikin wani mummunan artabu da ya yi sanadiyar mutuwar soja guda.

Tsohon shugaban kasar ya lura cewa da yawa daga cikin ‘yan Najeriya da suka hada da Shugaba Buhari, Gwamnonin jihohi da shugabannin jam’iyyun siyasa har ma da ‘yan kasashen waje sun je sun ziyarce shi, wasu kuma sun kira don nuna juyayi da kan yanayin harin.

Jonathan ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu buhari da su kama wadanda suka aiwatar da wannan harin da kuma tabbatar da cewa irin wannan harin kunar bakin wake bai sake faruwa ba a cikin harabarsa ko wani wuri a cikin kasar ba.