Uncategorized
Mumunar Hatsarin Mota Ya Dauke Rayuka 2 Da Jikatar Da Mutane 12 a Zamfara
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Rundunar Yankin jihar Zamfara, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu a wani hatsarin mota wanda ya yi sanadiyyar jikkata wasu mutane 12 tare da raunuka daban-daban.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Yasir Shehu, wanda ya ba da tabbacin lamarin, ya ce hatsarin ya faru ne a kan hanyar Gusau zuwa Futuwa a safiyar ranar Asabar.
A cikin bayanin sa ya kara da cewa hadarin ya shafi motoci uku, wata Honda, wani bas din Toyota, da Golf, inda ya kara da cewa mazaje 14 ne ke a cikin motocin duka da hadarin ya faru da su.
Shehu ya danganta lamarin da yawar gudu na wuce gona da iri, ya ce dukkan wadanda suka jikkata an garzaya da su zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Gusau don basu kulawa.
Ya kuwa gargadi masu motoci akan tuki mai hadari da suka hada da wuce gona da iri, a cewar “Irin wadannan gudun ne ke sanadiyar hadarin motoci a kan hanya”.