Uncategorized
Gombe: Dankwambo Ya Caji Membobin PDP Da Su ci Gaba da kasancewa Da Hadin Kai
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya tuhumi membobi na jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Gombe da su kasance da hadin kai.
Tsohon gwamnan jihar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron PDP a Gombe ranar Litinin din nan da ta gabata.
Dankwambo wanda tsohon mataimakinsa, Charles Iliya ya wakilta a jawabin, ya bayyana da cewa ayyukan raya kasa a jihar duk a karkashin gwamnatin PDP ne.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Nuhu Poloma, yayin da yake nasa jawabi ya bayyana cewa an kayar da PDP a lokacin babban zaben shekarar 2019 ne saboda sun ki sakacci da yawa.
Poloma ya kara da cewa har yanzu jam’iyyar na da karfi sosai a jihar, duk da kayen da aka yi masu a babban zaben.
Shugaban PDP din ya gargadi mambobin jam’iyyar da bayar da tikitin neman zabe ga daidaikun mutane da suka ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar koda aka kashe su a jam’iyyar.
Shi kuma Shugaban Jam’iyyar PDP a Bauchi, Hamza Akunya, yayin da yake magana ya ce jam’iyyar ta sha kaye a babban zaben saboda ayyukan wasu membobin jam’iyyar da wasu jam’iyyu.
Akunya ya lura cewa, mambobin jam’iyyar PDP da suka fice daga jam’iyyar nan ba da jimawa ba zasu dawo.
“Shawarata a gare ku ita ce ku samar da sahihan ‘yan takara ga zaben 2023 wadanda zasu iya kayar da ‘yan adawa daga wasu jam’iyyu,” in ji shi.
Wata tsohuwar ‘yar majalisar wakilai, Binta Bello, yayin da take magana ta bayyana cewa an gudanar da taron ne domin hadin kan mambobin jam’iyyar.
Bello wadda itace ta shirya taron ta kara da cewa dole ne membobin jam’iyyar su fahimci cewa har yanzu jam’iyyar tana da karfi a jihar Gombe kuma a shirye take ta taka rawar gani