Uncategorized
‘Yan Hisbah Sun Kame Wani Dan Sanda Da Wasu Mata Uku a Gusau
Hukumar Hisba ta jihar Zamfara ta bayyana kame wani jami’in ‘yan sanda da wasu mata uku da ake zarginsu da aikata muggan laifuka a wani otal da ke Gusau.
Shugaban hukumar, Dakta Atiku Zawuyya ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar hukumar ranar Litinin din nan da ta wuce.
Dakta Zawuyya ya bayyana da cewa an kama jami’in ‘yan sanda da ke aiki tare da ofishin‘ yan sanda ta Central Police Station da ke a Gusau tare da ’yan matan uku a wani ‘Otal, da zargin su da aikata laifin da suka saba wa ka’idar Sharia.
Zawuyya ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa daya daga cikin ‘yan matan uku da aka kama ta fito ne daga jihar Kaduna yayin da sauran biyun kuma ‘yan gida guda ne a Zamfara.
Shugaban ya ce hukumar sau da yawa ta gargadi masu kula da otal din kan amince da shigar da irin wadannan mutane a Otal din amma sun kasa bin ka’idoji da ke jagorantar gudanar da kasuwancin otal a jihar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) sun bayar da rahoton cewa, jami’an hukumar Hisba sun kame harda Manaja da ke kula da Otal din.
Zawuyya ya karshe da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan cikakken bincike. (NAN).