Connect with us

Labaran Nishadi

Dan Damben Najeriya da Birtaniya, Anthony Joshua Zai Mika Wa Shugaba Buhari Bel Dinsa

Published

on

Fitaccen babban dan damben Anthony Joshua zai gabatar da belitinsa ga Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa a lamarin sanarwar  ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja.

Laolu Akande, Mataimaki na Musamman (SSA) ga Shugaban kasa kan kafafen yada labarai da sanarwa, Ofishin Mataimakin Shugaban, ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai a fadar Shugaban kasa jawabi a madadin Ministan Wasanni, Sunday Dare.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta ba da rahoton cewa, bayanin ya fito ne bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Ko da shike, Akande ya ce har yanzu ba a tsayar da ranar gabatar da bel din ba.

Ministan Wasanni ya sanar da cewa Anthony Joshua zai gabatar da belinsa ga Shugaban kasar cikin ‘yan kwanaki kadan da nan.

Naija News Hausa ta tuno da cewa Joshua, dan danben Najeriya da Birtaniya din ya buge Dan dambe Amurka da Mexico, Andy Ruiz Jr. a wata fadar nuna gwani da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata a Saudiya.

Nasarar Dan Damben ya kai shi ga mayar da belitin kyautarsa (IBF, WBO, WBA da IBO) na gwanewa a filin Damben daga hannun Ruiz Jr. wanda dan damben Amurka din ya lashe a wata Yuni da ta gabata.