Connect with us

Labaran Nishadi

Takaitaccen Labarin Rayuwar Hafsat Idris (Barauniya)

Published

on

Jaruma Hafsat Ahmad Idris, wadda aka fi sani da kiranta Hafsat Idris, yar wasan fim ne a shafin masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.

Hafsat asalinta ‘yar jihar Kano ce, arewacin Najeriya. Amma an haife ta da kuma girmar da ita ne a Shagamu, jihar Ogun.

Tauraron Jarumar Hafsat Idris ya hasko ne da bayyanata a hadin fim da ta yi inda ta taka rawar gani cikin fim din mai taken ‘Barauniya’, wannan shirin ne fim na musanman da ya haskaka jarumar da kuma daukaka ta a harkar fim.

An zabi Hafsat a matsayin jarumar Kannywood da ta fi fice a shekarar 2017 daga kamfanin dilancin shiri ta City People Movie Awards.

Hafsat Ahmad Idris ta fara shirin fim ne a shekarar 2016 a fim din Barauniya, tare da jarumi Ali Nuhu.

Naija News Hausa bisa bincike ta fahimta da cewa jarumar ta shiga masana’antar kannywood ne bayan da ta gwada hannun ta a harkar kasuwanci. Takan yi tafiye-tafiye mafi yawan lokuta daga Oshogbo, jihar Osun zuwa Kano saboda kasuwanci.

Ko da shike, duk da cewa ta fi kyau a harkar kasuwanci, amma sha’awar Hafsat ta karkata ga zama ‘yar wasa.

Hafsat ita ma ta mallaki kamfanin shirya fina-finai da aka sani da Ramlat Investment, kuma ta fitar da fina-finai da dama a shekarar 2019 ciki har da fim mai ‘Kawaye’, babban shirin ya hada da manyan ‘yan wasa da shugabannai a Kannywood, kamar su Ali Nuhu, Sani Musa Danja, hadi da ita Hafsat.

Hafsat ta fice a cikin fina-finai da yawa, kamar su; Biki Buduri, Furuci, Labarina, Barauniya, Makaryaci, Abdallah, Ta Faru Ta Kare, Rumana, Da Ban Ganshi Ba, Wacece Sarauniya, Zan Rayu Da Ke, Namijin Kishi, Rigar Aro, Yar Fim, Dan Kurma, Kawayen Amarya, Dr Surayya, Algibla, Ana Dara Ga Dare Yayi, Mata Da Miji, Dan Almajiri, Haske Biyu, Maimunatu, Mace Mai Hannun Maza, Wazir, Gimbiya Sailuba, Matar Mamman, Risala, Igiyar, Zato, Wata Ruga, Rariya.