Connect with us

Labaran Duniya

‘Yan Bindiga Sun Kashe Firist Na Katolika A Katsina

Published

on

‘Yan hari da bindiga sun kashe wani babban firist na Katolika da aka bayyana da suna Rev Fr Alphonsus Bello.

Rahoto a yau Jumma’a ya bayyana da cewa an kashe malamin ne yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a cocin Katolika na Vincent Ferrer, Malunfashi, Jihar Katsina.

Wani malami a cocin, Dominic, wanda ya yi magana a kan lamarin, ya bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan bindigar sun hari cocin ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis. Dominic ya lura cewa nan da nan da su isar a ikilisiyar, sun hari dakin inda malamin yake ne suka yi wuf da shi.

Ya kara da cewa marigayin yayi kokarin bijire wa ‘yan bindigar amma da cewa sun sha karfinsa.

Naija News ta gane da cewa an tafi ne da marigayin tare da wani dattijo firist mai suna Rev Father Joe Keke, amma da baya an ga gawarsa a safiyar Juma’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Isah Gambo, yayin tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama mutane biyu.

Gambo kara da cewa ‘yan sanda suna bin sawun maharan.

Ka bi wannan shafin don samun karin bayani daga baya…