Connect with us

Labaran Nishadi

Atletico Madrid Ta Lashe La Liga

Published

on

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Atletico Madrid ta zama zakara a gasar La Liga ta Spain ta 2020/2021.

Naija News ta gane da cewa hakan ya faru ne bayan kulob din ta yi nasara da dukar Real Valladolid a ranar Asabar da gwalagwalai 2-1.

Oscar Plano ne ya fara yaga ragar Madrid a minti na 18 kafin Angel Correa ya rama wa Madrid da gwal a minti na 57.

Dan kwallon Madrid, Luis Suarez, ya tallafa wa kulob dinsa da gwal a bayan minti 10 tsakani, kwallon da aka gama da gwalagwalai 2-1.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa manajan Liverpool, Jurgen Klopp, ya dage cewa da kocin Manchester City, Pep Guardiola bai lashe gasar Premier ta bana ba idan da ‘yan wasan sa na tsakiya uku sun ji raunuka kamar ‘yan wasan Liverpool.

Klopp ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai kafin wasan da Liverpool za ta kara da Crystal Palace ranar Lahadi din nan.