Connect with us

Labaran Nishadi

Daraktan Nollywood, Abiodun Aleja Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Published

on

Sanannan dan wasan kwaikwayo na Najeriya da kuma darakta a Nollywood, Abiodun Aleja, ya mutu.

Rahoton da ke isa ga Naija News a wannan sa’a ta bayyana da cewa Aleja ya mutu ne a Legas ranar Juma’a.

Ya yi aiki a kan ayyuka da dama tare da abokan aiki kamar su Tunde Kelani da Kunle Afolayan.

Za a tuna da mamacin saboda rawar gani da ya taka a finafinan Afolayan na ‘1 ga Oktoba’.

Shugaban kungiyar ‘National Theater of Nigerian Theater Arts Practitioners (NANATAP)’ reshen Legas, Makinde Adeniran, ya ce matar mamaicin ne ta sanar da labarin.

Rahoto ta bayar da cewa an kwantar ne da Aleja a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH) bayan ya fadi a gidansa makonni da suka gabata.

An rahoto cewa jarumin fim din ya shiga halin ha’ula’i amma an sake farfaɗo da shi a asibiti. Hakika ya mutu ne bayan da ake tsamanin ya fara samun sauki.