Connect with us

Labarai Hausa

Gawar Marigayi Attahiru Da Sauran Hafsoshin Soja Ya Iso Abuja Don Jana’izar

Published

on

Gawar babban hafsan sojan kasa ta Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru da sauran hafsoshi da suka mutu a hatsarin jirgi sama Beachcraft 350 a filin jirgin saman Kaduna ranar Juma’a sun isa Abuja.

Naija News na sanar da cewa jami’an sojojin a fadar shugaban kasa na Filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja, sun karbi gawakin ne da misalin karfe 11 na safiyar Asabar.

An kuma dauke su zuwa Babban Masallacin Abuja da Cocin Furotesta da ke sansanin sojojin sama, Abuja.

Karin labarai na tafe a sannu…