Connect with us

Labarai Hausa

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Korar Malamai Da Basu Cancanta Ba A Makarantu

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dage da cewa zata kori dukan malaman da ba su cancanta ba a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu a duk fadin kasar.

Naija News ta fahimci cewa kudrin ya biyo ne bayan da malamai 17,141 a duk faɗin jihohi Najeriya 36 hadi da babban birnin Tarayya, FCT, suka rubuta Jarrabawar wararriya wadda kungiyar Rajistar Malamai ta kasar ta shirya.

Da yake lura da jarabawar a Abuja, Babban Sakatare, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Sonny Echono, ya bayyana cewa matakin ya zama dole ne don tabbatar da kwarewa a layin samar da ilimi a kasar.

Ya ce bai kamata a dauke mutane ba tare da cancantar koyarwa ba a matsayin malamai.

Bayanin Echono na kamar haka: “Mun fara aiwatar da manufar tabbatar da cewa kwararrun malamai ne kawai za su kasance a dukkan makarantunmu kuma daga nan za mu koma makarantu masu zaman kansu.

“Mun rigaya mun fara tattaunawa mai armashi tare da shugabannan makarantun jihohi da kuma makarantu masu zaman kansu don tabbatar da cewa an yi hakan saboda wannan ita ce babbar jarin da za ku iya samarwa ga kasar ku ta nan gaba don tabbatar da cewa sun sami ilimi mai inganci.

Ya kara da cewa yadda ake gudanar da jarrabawar ba shi da kyau bisa gabatarwar na’urar fasaha.

Echono ya kuma bayyana cewa ma’aikatar na aiki tare da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki, Hukumar Kula da Shaida ta Kasa da sauran hukumomin da ke samun bayanai don samun halin da za a ajiye asalin yaran firamare da zaran sun yi rajista a kowace makaranta a kasar. .

Ya kuma yi magana game da sabon tsarin albashin da aka amince da shi ga malamai.

“Ku gane da cewa mun fara aiwatar da wannan, muna aiki tare da shugabar ma’aikatan kuma ta kasance mai adalci da matukar taimakawa don tabbatar da biyan ma’aikata da kuma albashi yayin da muke magana, muna kirga wadancan alawus din na karkara, alawus din kimiyya, hadari da sauransu. don tabbatar da cewa malamai sun samu ladarsu a nan duniya ba lahira ba,” inji shi.

Mai rikon mukamin Darakta a majalisar rajistar malamai a Najeriya, Mrs Jacinta Ogboso, ta bayyana cewa kimanin dalibai 17,141 ne za su halarci jarabawar ta Batch A a duk fadin kasar.

Ta kuma bayyana cewa jihar Osun ce ke da adadi mafi yawa yayin da ta kara da cewa za a magance bukatun malaman da ke da bukata ta musamman.

“Batun mutane masu bukata ta musamman a tsakanin malamai wannan abu ne da ba za a iya yin watsi da shi ba. Koyaya, akwai wasu lamuran da mutum ba zai iya farkawa da mu’amala da su ba a cikin kwana ɗaya kawai.

“Mun fara aikin magance su, gano su da sanin su. Mun riga mun fara tattaunawa da cibiyoyin da suka kware a wannan fannin kamar Kwalejin Ilimi ta Tarayya,” in ji ta.