Connect with us

Labarai Hausa

Kalli Hotuna Daga Jana’izar Marigayi Attahiru Da Sauran Hafsoshin Sojojin Najeriya

Published

on

A yau Asabar, 22 ga watan Mayu ne za a yi hidimar jana’izar babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan hafsoshi shida da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ta bayyana cewa za a binne su a makabartar sojoji da ke Abuja.

Ya kara da cewa za a gudanar da sallar Jana’iza da addu’o’i a lokaci daya a Babban Masallacin Juma’a na Abuja. Haka kuma za a gudanar da addu’a a National Ecumenical da ke Abuja ga wadanda abin ya shafa.

Naija News ta kula da cewa jana’izar ta kunshi hafshoshin Musulmi shida ne daga cikin jami’ai 11 da suka rasa rayukan su a hatsarin jirgin a ranar Juma’a, ciki har da janar-janar hudu.

Sauran sojojin da suke zaman kiristoci za a binne su gwargwadon imanin addininsu.

Kalli hotuna a kasa a yayin da aka rigaya da fara hidimar jana’izar a birnin Abuja.