Connect with us

Labaran Nishadi

Man City Ba Zai Lashe Gasar Premier Ba Idan Da ‘Yan Wasan Na Da Raunuka – Klopp

Published

on

Manajan Liverpool, Jurgen Klopp, ya dage cewa da kocin Manchester City, Pep Guardiola bai lashe gasar Premier ta bana ba idan da ‘yan wasan sa na tsakiya uku sun ji raunuka kamar ‘yan wasan Liverpool.

Naija News ta gane da cewa Klopp ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai kafin wasan da Liverpool za ta kara da Crystal Palace ranar Lahadi din nan.

Ku tuna da cewa Liverpool ta yi wasanan bana ne ba tare da mai tsaron bayansu ba, watau Virgil van Dijk, sabili da raunin da ya samu a shekarar da ta gabata. Haka kazalika Joe Gomez ya yi jinya jim kadan bayan haka tare da raunin gwiwa kafin Joel Matip ya zama na uku da ya dade yana rauni a tsakiya.

“Don haka kungiyar kwallon kafa kamar kungiya ce ta kade-kade inda mutane da yawa ke aiki tare, kuma idan aka rasa guda daya, za ku iya ci gaba da yin ta, amma idan rashi ta zama biyu, to ya zama da wahala,” in ji Klopp ga Sky Sports.

Ya kara da cewa: “Yadda na ce ne kafin wannan shekarar, tare da yawan raunin da muka samu, wannan shekarar ba ta neman zama zakaru ba, babu damar haka,”

“Kamar yadda suke da kyau, idan [Manchester] City ta fitar da tsakankaninta guda uku, a’a [ba su lashe gasar ba]. Uku-rabi-biyu na United, a’a. Ga dukkan tsawon lokacin, kyawawan abubuwa ma, wannan shine yadda yake.

“Mun yi gwagwarmaya kadan, mun yarda da matsalolin kuma mun yi mafi kyau da ita, kuma idan muka yi nasara ranar Lahadi, kuma idan har mun tsallake zuwa Kofin Zakarun Turai, to mun yi mafi kyau da shi. Wannan kenan.”

Naija News ta fahimci cewa kungiyar kwallon Liverpool a halin yanzu tana matsayi na hudu a kan teburin Premier kafin karawar karshe ta kaka da Crystal Palace wannan Lahadin.