Connect with us

Labarai Hausa

Shirye-Shiryen Jana’izar Marigayi Babban Hafsan Sojoji A Masallacin Abuja

Published

on

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa za a yi jana’izar babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan hafsoshi shida da suka mutu a hatsarin jirgin sama da ya afku a Kaduna ranar Juma’a.

A wata sanarwa da aka bayar ‘yan sa’o’i da suka gabata, rundunar sojoji ta sanar da cewa zana’izar sai kasance ne da yammacin ranar Asabar, 22 ga watan Mayu, 2021.

Rahoton ta kara da cewa za a yi jana’izar ne da missalin karfe 12:30 maimakon 10:00 na safe kamar yadda aka sanar a baya.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ta ce za a binne su a makabartar sojoji da ke Abuja.

Za a gudanar da sallar Jana’iza da addu’o’i a lokaci guda a Babban Masallacin Juma’a na Abuja. Haka kuma za a gudanar da addu’a a National Ecumenical da ke Abuja ga wadanda abin ya shafa.

Kalli hotuna a kasa a yayin da ake shirye-shiryen jana-izar: