Connect with us

Labaran Nishadi

Tsohon Golan Barcelona, Francesc Arnau Ya Mutu

Published

on

An sanar da mutuwar tsohon golan ‘yan kwallon kafa ta Barcelona, Francesc Arnau.

Rahoton da ke isowa ga Naija News a wannan lokaci ta bayyana da cewa Arnau ya mutu ne a safiyar Asabar, 22 ga watan Mayu.

Kulob din Sifen, Real Oviedo, ne ta tabbatar da mutuwar tasa a cikin wani sako da suka wallafa ta shafinsu na Twitter a yau Asabar.

An bayyana da cewa Arnau ya mutu ne yana shekara ta 46.

“Daraktan wasanninmu, Francesc Arnau Grabalosa, ya riga mu gidan gaskiya,” sakon da aka samar a layin Twitter na Real Oviedo na kamar haka.

“Muna matukar nadamar rashinta kuma mun raka iyalanta cikin wadannan mawuyacin lokaci. Ka huta lafiya.”

Naija News ta gane da cewa Arnau yana aiki ne a matsayin Daraktan Wasanni a Real Oviedo tun Disamba 2019.

Ya fara aiki ne da kulob na matasan Barcelona, ya kuma ci gaba da aikin sa ne gaba da burin cinma kungiyar farko, inda ya kwashe shekaru uku daga 1998 zuwa 2001.

Tsohon dan wasan ya bar Barcelona ne a shekara ta 2001 ya koma Malaga.