Connect with us

Labaran Siyasa

Gwamnonin PDP Sun Nuna Damuwa Ga Binciken EFCC Kan Kudaden Jam’iyyar

Published

on

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar adawa, (PDP-GF) a ranar Asabar, 22 ga watan Mayu, 2021, sun nuna damuwa kan matakin da Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta dauka don binciken asusun jam’iyar.

Kungiyar a cikin wata sanarwa daga Babban Darakta, Mista CID Maduabum, a Abuja, ta ce PDP na da cikakken rahoton asusun ajiyarta na shekara-shekara ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.

Maduabum ya ce gwamnonin PDP ba su da masaniya cewa INEC ta yi wani korafi ga EFCC kan zancen kudaden jam’iyar.

Ya ce gayyatar da jami’an EFCC suka yi wa jami’an PDP ya kawo wasu damuwa a kan rashin nuna wariyar hukumar ta cin hanci da rashawa. Maduabum ya ce PDP a matsayinta na jam’iyyar siyasa tana da amana ga mambobinta da sauran jama’a kan ayyukanta.

“Gwamnonin PDP sun damu matuka cewa hakan wani fifiko ne mara kyau kuma ya sa aka dakatar da adawar siyasa,” in ji shi DG.

Ya shawarci sabbin shugabannin EFCC da suyi koyi da kuskuren magabatansu.

“Korafin da ake ma magana a kai bai bayyana wani zargi ba na amfani da kudaden gwamnati ba, ko yaudarar wani mutum ko wata hukuma ta PDP.

“Don haka, abin mamaki ne a ce ya kamata EFCC ta yi amfani da karancin dan Adam da sauran kayan aikinta don fara bincike kan kudaden PDP. “Idan har EFCC na hannu-biyu kuma ba na bangaranci, ya kamata kuma ta gudanar da bincike a kan wasu jam’iyyun siyasa ciki har da jam’iyya mai mulki,” in ji Maduabum.