Connect with us

Labaran Siyasa

Jerin Gwamnonin Da Suka Halarci Daurin Auren Dan Malami

Published

on

Wasu gwamnoni Jihohin Najeriya da ma’aikatan gwamnati a wannan karsheh makon, sun halarci bikin dan Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a.

Naija News ta ruwaito da cewa gwamnonin sunyi watsi ne da kasance wurin jana’izar jami’an Sojojin Najeriya da suka mutu hadi da Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan sojojin Najeriya.

Ka tuna da cewa Attahiru da hafsoshi 10 din sun mutu ne a hatsarin jirgin sama da ta faru a Jihar Kaduna kwana biyu da suka gabata.

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da nuna bakin ciki da rasuwar, gwamnoni da ma’aikatan gwamnatin sun rabu kashi biyu, wasu sun kasance wurin jana’izar jami’an da haka kazalika wasu sun zabi girmama zuwa wurin bikin auren dan Malami.

Kalli hotuna a kasa:

Ga sunayan gwamnonin da manyan ma’aikata da uka halarci auren dan Malami da kuma jana’izar a kasa:

1. Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle

2. Aminu Tambuwal na jihar Sokoto

3. Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe

4. Abdullahi Ganduje na Kano

5. Atiku Bagudu na Kebbi

Wadanda suka halarci jana’izar sune:

1.Gwamnoni Babagana Zulum na jihar Borno

2. Nasir El-Rufai na jihar Kaduna

3. Mai Mala Buni na Yobe

Sauran jami’an gwamnatin sun hada da:

1. Lai Mohammed – Ministan Yada Labarai

2. Bashir Magashi – Ministan Tsaro

3. Farfesa Ibrahim Gambari – Shugaban Ma’aikata na Shugaba Muhammadu Buhari

4. Janar Lucky Irabor – Shugaban hafsoshin tsaro

5. Rear Admiral Awwal Gambo – Shugaban hafsan sojan ruwa

6. Mukaddashin IGP, Usman Baba.

Hakika, a halin yanzu, ‘yan Najeriya ba su gamsu da ci gaban ba, wasu mutane da yawa suna sukar gwamnonin.