Connect with us

Labaran Siyasa

Oyo: OYSIEC Ta Sake Daga Zaben Karamar Hukumar Ido

Published

on

Hukumar gudanar da hidimar zabe a Jihar Oyo (Oyo State Independent Electoral Commission – OYSIEC), ta sake dakatar da zaben karamar hukumar Ido, daya daga cikin kananan hukumomin da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Naija News ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na biyu da hukumar zabe ke dakatar da zaben a Ido, wanda shi ma yana daya daga cikin kananan hukumomi tara da ke gundumar Sanatan Oyo ta Kudu.

Wakilin gidan labaran Daily Post ya ruwaito an dakatar da zaben ne wanda ya gudana a dukkan kananan hukumomi 33 na jihar. Kanfanin dilancin labaran mu ta fahimci cewa an dakatar da zaben ne sakamakon watsi da tambarin Zenith Labour Party (ZLP) a takardun zaben ranar Asabar da ta gabata.

Daga baya an sake sanya ranar zaben zuwa yau (Lahadi). Wakilinmu ya ruwaito cewa a haka an sake dakatar da zaben.

Shugaban OYSIEC, Barista Isiaka Olagunju, ya sanar da dakatar da zaben a ranar Lahadi. Olagunju, duk da haka, ya ce za a gudanar da zaben ne a ranar Asabar mai zuwa, 29 ga Mayu 2021.

Wakilinmu ya samu labarin cewa a yanzu haka OYSIEC na sanar da sakamakon zabukan kananan hukumomi a sauran ragowar kananan hukumomi 32 da zaben ya gudana.