Connect with us

Labaran Siyasa

Wariyar Da A Ke Wa Kudu-Maso-Gabas Laifin Shugabanni Yankin Ne – Tsohon Sanata, Anyanwu

Published

on

Tsohon Sanata wanda ya wakilci gundumar sanata-ta-gabas, Samuel Anyanwu, ya zargi shugabannin Kudu Maso Gabas da sanadin ci gaban wariyar da ake wa Ndigbo a Najeriya.

Naija News ta ruwaito da cewa dan majalisar ya zargi shuwagabannin da kasancewa marasa yada yawu wajen zancen takara.

A wata sanarwa da ya baiwa manema labarai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ikenna Onuoha, ya nuna damuwar cewa wadanda ake sa ran za su yi magana a kan nuna wariyar launin fata ga ‘yan kabilar Ibo da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi, sun gwammace su mayar da kansu kayayyakin aiki ne kawai ga shugabancin kasar a karkashin Buhari.

“Aiki ne na matsoraci, mugunta da rashin kyautatawa mutanenmu cewa waɗanda ake tsammanin yin magana suna ɓoyewa suna ɓoye kansu a ƙarƙashin gaskiyar yanzu.

“Ya kamata su rufe fuskokinsu cikin jin kunyar cewa wasu shiyyoyi suna ci gaba yayin da yankinsu ke baya.

Ta kara da cewa “Har sai shugabannin yankin kudu maso gabas sun fara magana da murya daya, shiyyar za ta ci gaba da kasancewa mara ci gaba.”

Sanarwar ta kara danganta neman warewar kasa da wasu kungiyoyin ‘yan awaren ke yi a yankin da yawan rashin daidaito na siyasa, wulakanci da watsi da gwamnatin mai ci ke yi wa yankin.