Connect with us

Labarai Hausa

An Toshe Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Da Zanga-Zanga Kan Sace Mutane 30 Da ‘Yan Fashi Suka Yi

Published

on

Rahoto da ke isowa ga Naija News a wannan lokaci ya nuna da cewa wasu mazauna garin Gauraka, karamar hukumar Tafa, a jihar Neja, a safiyar Litinin sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da zanga-zanga.

Mazaunan sun fito ne da yawan su don nuna rashin amincewa da jerin sace-sacen da akeyi a yankin su.

Naija News ta kula da cewa Garin Gauraka yana kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ne. Zanga-zangar da aka fara a safiyar yau ya dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar yayin kona tayoyi da ‘yan zanga-zangar ke yi kan babban titin.

Al’umar na gudanar da zanga-zangar ne saboda sace wasu mazauna garin da ‘yan bindiga suka yi sa’o’i da suka gabata.

Sun ce kimanin mutane 30 daga cikin al’umar na cikin matattarar ‘yan bindigar wadanda ke neman a biya su kudin fansa mai tsoka.

Masu zanga-zangar sun ce sun fara wannan fitar kishi ne domin kiran hankalin hukumomin da abin ya shafa kan halin da suke ciki bayan ‘yan bindigar suka mamaye garin a ranar Litinin da misalin karfe 1:00 na safe suka yi awon gaba da mutane 15.

Da yake magana yayin zanga-zangar, wani dan yankin wanda ya bayyana kansa a matsayin Hassan Hassan ya ce ‘yan bindigar sun mamaye yankin da misalin karfe 1:17 na safe sannan suka yi awon gaba da mutane 15.

Ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zangar ne don neman gwamnati ta kawo musu dauki a jihar Neja.

“Da karfe 1:17 na safe na ji karar harbe-harbe. Dole ne na hanzarta da rufe tagogina saboda a buɗe suke. Na fada wa mutanena a gida da su kwantar da hankulansu,” inji shi.

“Na shiga dakin yin bayi na gida na don ganin abin da ke faruwa. Na ga cewa ‘yan bindigan sun tafi da makwabcina tare da yaransa biyu. Daya yana da shekara 10 kuma na biyun yana dan shekara 8.

“Sun aikatar da harin ne har zuwa kusan 1:51 na safe. Da misalin karfe 2:15 na safe, sojojin suka kawo mana dauki. Wasunmu sun fito domin ganin wadanda aka sace. Mun gano cewa sun yi garkuwa da mutane kusan 15 kuma sun yanke hannu biyu da kunnen wata mata wacce ke dauke da jariri.

“Wannan ba shine karo na farko ba. Wannan ba shine karo na biyu ba. Muna so kawai mu sani ko muna cikin aminci a kasar nan da kuma Najeriya. 

Wani dan yankin, wanda ya bayyana kansa a matsayin Dare ya ce a ranar Alhamis din da ta gabata ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane hudu a yankin kuma suna neman kudin fansa na Naira miliyan 10.

Ya ce lokacin da jama’ar suka sanar da wani ofishin ’yan sanda da ke kusa da lamarin, sai aka shaida musu cewa babu alburusai da abin hawa da za su iya dakile harin.