Connect with us

Labarai Hausa

Babbar Mota Ta Murkushe Mutane Uku Har Lahira A Ogun

Published

on

Wata babbar mota da ke kan tafiya a kan hayar da ke kusa da Ago Oko a Abeokuta, a ranar Lahadi ta kashe wasu mutane uku da ke kan babur.

Mista Babatunde Akinbiyi, mai magana da yawun rundunar, Ogun Traffic Compliance and Enforcement Corps (TRACE), wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da karfe 8 na daren Lahadin da ta gabata.

Akinbiyi ya bayyana cewa, mahayin babur din yana kokarin ne ya tsere babban motar daga hannun dama, yana mai cewa a cikin hakan ne ya yi karo da wani babur din da ke kan gudu wanda ya jefa su a karkashin babban motar.

“Mun tattara ne daga wanda ya gana da faruwar cewa babur din yana kokarin wuce wata motar Dangote ne daga hannun dama, sai dai kash wata babur da ke tafe a baya da gudu ya yi karo da babur din wadanda lamarin ya rutsa da su, haka dukan su suka fada a karkashin babbar motar da ke tafiya a kan layin.

“Su ukun da suke kan babur din a take suka murkushe har lahira a yayin hadarin.”

Akinbiyi ya kara da cewa “An yi amfani da wayar da aka gano a wurin don danganta da dangin mamacin kuma danginsu sun isa wajen on daukar gawarwakin.”

Ya ce har yanzu, babbar motar tana wurin da hatsarin ya afku, yana mai cewa wasu ‘yan iska sun yi amfani da damar wajen sace kayakin da a cikin motar bayan sun fatattaki ‘yan sanda da jami’an TRACE daga wurin.