Connect with us

Labarai Hausa

Buhari Ya Ayyana Ranar Litinin Ga Hutun Aiki Don Rasuwar Attahiru

Published

on

Ranar Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana Litinin, 24 ga Mayu a matsayin ranar hutu daga aiki ga Sojojin kasar domin karrama marigayi Babban hafsan Sojojin, COAS, Ibrahim Attahiru.

Buhari ya kuma bayar da umarnin cewa a sauke tutar Najeriya kasa-kasa a duk fadin kasar.

Naija News ta ruwaito da cewa sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha ne ya bayyana umarnin shugaban kasa a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadi.

Sanarwar ta ce: “Mai girma, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da izini cewa a sanya Tutar Najeriya kasa-kasa a dukkan fadin kasar daga ranar Litinin 24 ga Mayu zuwa Laraba 26 ga Mayu, 2021.

“Umarnin ta kasance ne don karrama marigayi babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, da sojoji goma da ke yi wa kasar hidima wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman ranar Juma’a.

“Hakazalika Shugaban kasa ya amince da ranar Litinin, 24 ga Mayu, 2021 a matsayin ranar hutun aiki ga rundunar Sojojin kasar.”

Naija News ta ruwaito da cewa Attahiru da wasu jami’ai 10 sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama da yammacin ranar Juma’a a jihar Kaduna.

Babban hafsan sojan tare da mukarrabansa suna kan aikinsu ne zuwa jihar a lokacin da hatsarin ya faru a filin jirgin saman Kaduna.

Rundunar sojoji a ranar Asabar ta isar da gawar Attahiru da sauran jami’an da suka mutu zuwa Abuja domin yin jana’izar su duka.