Connect with us

Labarai Hausa

Jamhuriyar Oduduwa: Tinubu, Gbaja, Gwamnonin APC Sun Ki Amince Da Sunday Igboho

Published

on

Wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Kudu maso Yamma ba su nuna rashin amincewa da Sunday Adeyemo (Sunday Igboho) kan kiran da ya yi ga neman kafa kasar Yarbawa ba.

Naija News ta ruwaito da cewa shugabannin sun hada da shugaban jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu, Bisi Akande, Segun Osoba, Gwamnan jihar Lega, Babajide Sanwo-Olu, Dapo Abiodun (Ogun), Gboyega Oyetola (Osun), Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Shugabannin sun hadu ne a ranar Lahadi a gidan gwamnati, Marina, Legas don tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da yankin ke fuskanta da ma Najeriya baki daya, in ji Gov Abiodun.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron ta sanar da cewa shugabannin APC sun nuna “adawa mai karfi ga masu neman ballewa da kalaman nuna kiyayya.”

Ka tuna da cewa Sunday Igboho ya kasance jagora a kan hargitsi na neman kafa Jamhuriyar Oduduwa, yayin da ya jagoranci magoya bayansa zuwa Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Asabar don wani taron gangami.

Igboho ya sha suka a lokuta da dama a kan tsokaci kan masu adawa da gwagwarmayar sa ga neman kafa Jamhuriyar Oduduwa.

Shugabannin na APC, yayin da suke kwatanci da Sunday Igboho da abokan tafiyarsa, sun bukaci “wadanda ke kokarin tayar da zama tsaye su hanzarta, su sabunta imaninsu game da hadin kai, kwanciyar hankali da dorewar kasar.”

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Gwamna Abiodun ya ce, “Kudurin da aka cimma a muhimmin taron ya nuna rashin amincewa mai karfi kan neman ballewar kasar,”

“Ya kara da cewa taron ta nemi samar da kudaden ciyarwa ga Sojojin Najeriya, neman tsarin tarayya na gaskiya don ci gaba, kuma ya amince da kudurin na Mayu Taron Gwamnonin Kudu 11 da aka gudanar a Asaba.”