Connect with us

Labaran Nishadi

Kannywood: Kalli Sabbin Hotunan Rahama Sadau

Published

on

Duk da kalubalai da ta fuskanta, Jaruma Rahama Sadau, har ila yau ta kasance daya daga cikin shahararrun mata a shafin shirin fina-finan Hausa.

Naija News ta fahimci cewa Sadau shekara da ‘yan wattannai da suka gabata ta fuskanci kalubalai da dama a kan tsarin salon sa tufafin ta.

Wannan kamfanin dilancin labarai ta mu ta sanar a baya da cewa anyi gwagwarmaya da daukar mataki kan Sadau bayan da aka gano wasu hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, inda jarumar ke cikin wani yanayi da shiga marar kyan gani na rashin da’a, tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019; ya ce kungiyar na fuskantar matsala game da daukar mataki kan jarumar, Rahama Sadau.

A yanayin da ya bayyana da mara kyan gani da kuma abin kyama wacce yake zargin jarumar ta yi akan ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.

Rahama Sadau da mawakin Hiphop, Falz

Sadau a yayin mayar da martani a wannan lokacin, ta ce shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.

Duk da wadanan, Sadau bata raunana ba a yayin da ta ci gaba da hidimar sana’ancinta da sauran al’amurori ba tare da kulawa da wata jita-jita ko kishi ba.