Connect with us

Labaran Siyasa

OYSIEC Ta Mikar Da Satifiket Ga Zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi 32

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Oyo (OYSIEC) a ranar Litini, 24 ga Mayu, ta gabatar da satifiket na komawa shugabanci ga dukkan zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa OYSIEC a ranar Lahadi ta bayyana ‘yan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party da lashe kujerar shugabancin kananan hukumomi 32 daga cikin 33 a zaben da aka kamala a jihar.

Ku tuna da cewa zaben kananan hukumomin jihar ta gudana ne a ranar Asabar da ta gabata. An gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 32 cikin 33 da ke jihar a yayin da aka tsayar da daga zaben karamar hukumar Ido zuwa ranar Laraba, 26 ga Mayu 2021.

Shugaban OYSIEC, Barista Isiaka Olagunju ya gabatar da satifiket din dawowa ga dukkan zababbun shugabannin kananan hukumomin ne ranar Litinin. Olagunju, yayin gabatar da takardun shaida, ya shawarci zababbun shugabannin kungiyar da su cika dukkan alkawuran da suka dauka wa mutanen da suka zabe su.

Ya bukace su da suyi aiki domin barin abubuwan tarihi masu dorewa a majalisunsu.

Ya ce: “Ina so su ga kansu a matsayin bayin mutane. Ya kamata su yi aiki tare da tabbatar da cewa sun bar abubuwan tarihi masu dorewa.”

“Ya kamata su cika alkawuran da suka yi wa mutane,” in ji Olagunju.