Connect with us

Labaran Siyasa

PDP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Oyo

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Oyo ta bayyana ‘yan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party da lashe kujerar shugabancin yanki da kananan hukumomi 32 daga cikin 33 a zaben da aka kamala a jihar.

Naija News ta ruwaito da cewa shugaban OYSIEC, Mista Isiaka Olagunju (SAN), ya bayyana wadanda suka yi nasarar ne a hedkwatar hukumar da ke Ibadan ranar Lahadi.

Ku sani da cewa akwai kananan hukumomi 33 a jihar, amma an dakatar da zaben a Karamar Hukumar Ido a ranar Asabar saboda bin ka’ida game da watsi da tambarin Zenith Labour Party da aka yi a takardun jefa kuri’a a majalisar.

Olagunju ya fada a ranar Asabar cewa hukumar ta dauki alhakin kuskuren kuma ta dage zaben yankin zuwa Lahadi (washegari).

Yayin da zaben ya kasa gudana a ranar Lahadi, shugaban OYSIEC ya sanar da cewa za a gudanar da zaben a ranar Asabar, 29 ga Mayu, watau a karshen wannan sabuwar makon.

Ganin cewa ranar 29 ga watan Mayu hutu ce ta jama’a, sai ya sake canza ranar zuwa Laraba, 26 ga Mayu. Akwai jita-jitan cewa an kashe wani kuma an kone motoci biyu, amma ba a iya tabbatar da hakan nan take.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Oyo, Mista Adewale Osifeso, ya ce an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali, duk da cewa gwamna Seyi Makinde ya nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben.