Connect with us

Labarai Hausa

Shehu Sani Ya Yada Yawu Kan Zanga-Zangar Mutanen Neja A Abuja

Published

on

Tsohon Sanata wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a jagorancin Sanatoci na 8 na Najeriya, Shehu Sani, ya yada yawu kan zanga-zangar da mazauna garin Gauraka, karamar hukumar Tafa, a jihar Neja suka yi a yau Litini.

Naija News ta ruwaito ‘yan sa’o’i da suka wuce da cewa mazaunan yankin Neja a safiyar Litinin sun toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da zanga-zanga.

Mazaunan sun fito ne da yawan su don nuna rashin amincewa da jerin sace-sacen da akeyi a yankin su. Al’umar na gudanar da zanga-zangar ne saboda sace wasu mazauna garin da ‘yan bindiga suka yi sa’o’i da suka gabata.

Yayin yada yawun sa a kan batun, Sanata Sani a wata sako a hanyar yanar gizon ta Twitter a yau, ya jinjina wa sojoji mata da aka tura watannan baya don tsaron mutanen.

Ya ce: “Mutane sun yi tururuwa a kan hanyar Kaduna da ke Abuja don nuna rashin amincewa, bayan sace mutane goma a kan hanyar a jiya. Matan sojoji da aka tura watanni baya ana ganin kamar ba su da tsaro, amma suna yin aiki fiye da maza.”

“Na gumanci su kare gonata a can.”

Ga zancen Sanata Sani a kasa kamar yadda ya samar a turance a layin Twitter: