Connect with us

Labaran Siyasa

Babu Ja Da Baya Kan Kudurin Mu Game Da Kiwon Shanu A Fili – Okowa

Published

on

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya mayar da martani game da furucin da fadar shugaban kasar ta yi wanda ya saba wa kudurin gwamnonin Kudu akan rashin amincewa da kiwon shanu a yankin.

Naija News ta ruwaito da cewa fadar shugaban kasa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana kudurorin gwamnonin yankin a matsayin “ayyukan siyasa da masu sanya hannu suka nemi nuna fifiko da iko.”

Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, a wata sanarwa da ya fitar, ya la’anci gwamnonin, da cewa mataki da yunkurin su keta ne da neman toshe hakkin wasu ‘yan Najeriya

Yayin da yake maiyarda martani game da ikirarin fadar shugaban kasa, Gwamna Okowa wanda shine Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Kudu, ya ce babu gudu ba ja da baya kan kudurin da aka cimma kwanan nan a Asaba, babban birnin jihar Delta.

A wata sanarwa daga Babban Sakataren sa na yada labarai, Mista Olisa Ifeajika, Okowa ya ce gwamnonin basu damu ba da duk wata zancen fadar shugaban kasa a kan lamarin.

Ya ce, “Sun ce aikin siyasa ne don haka me? Idan suna so su kira shi siyasa, ba wani abu bane a gare mu.”