Connect with us

Labaran Nishadi

Barcelona Ta Bukace Ni Da In Roki Messi Ya Tsaya A Kulob Din – Suarez

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Luis Suarez, ya yi ikirarin cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bukace shi da ya roki dan wasan Argentina, Lionel Messi, lokacin da yake son barin bazarar da ta gabata.

Naija News ta ruwaito da cewa Suarez wanda ya bar Nou Camp a bara bayan da ya rattaba hannu ga zuwa Atletico, inda ya ci kofin laliga a kakar 2020/2021, ya zargi manajan Barcelona na yanzu, Ronald Koeman, da rashin ‘hali mai kyawo’.

Suarez ya fusata cewa tsohon shugaban Barcelona, ​​Josep Bartomeu, bai kasance da karfin gwiwar yi masa magana ba lokacin da kulob din ke son ya tafi gaba.

Dan wasan mai shekara 34 ya fada wa El Partidazo de COPE da cewa: “Ba zan taba yin gaba da Barcelona ba, sun ba ni komai kuma sun ba ni damar zuwa wurin fitattun ‘yan wasa, amma a bayyane yake cewa shugaban kulob din na da, Josep Maria Bartomeu, ya yada yawun sa duka ga manema labarai maimakon kirana.”

“Lokacin da suke neman Leo [Messi] da ya tsaya sun kira ni don amfani da ni don shawo kansa, don yin magana da [Antoine] Griezmann… To me yasa basu kira ni ba yayin da suke son in tafi?” Suarez yayi wannan bayani ne da manema labaran wasa.

“Ko me ya sa kocin bai zo ya gaya min cewa bai dogara da ni ba saboda yana son wani dan wasan gaba?

“Koeman ya ce min bana cikin shirinsa, sannan ya ce: “Idan ba mu shan kan wannan zancen ba zuwa gobe, zaka komo cikin shirye-shiryena kuma ina dogaro da kai a wasan mu da Villarreal”.

“Daga nan na ga cewa mutumin ba shi da hali. Ba shi da ƙarfin da zai gaya mini cewa ba a buƙata na. Shawarar sayarwar da ni ta fito ne daga hukumar kulob din”, inji Suarez.