Connect with us

Labaran Siyasa

COAS: Ka Bar Dan Kabilar Igbo Ya Maye Gurbin Attahiru – Omokri Ya Gayawa Buhari

Published

on

Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya wani dan kabilar Igbo ga maye gurbin marigayi babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Ku tunda da cewa an ruwaito da baya da cewa Attahiru ya mutu ne tare da wasu hafsoshin soja a wata hatsarin jirgin sama kusa da Filin jirgin Kaduna a ranar Juma’a.

Manyan jami’ai din sun rasa rayukan su ne a lokacin da jirgin sama din mai lauyin lamba 350 ‘ya sauka dole saboda rashin kyawun yanayi.

Naija News ta kula da cewa har yanzu, Buhari bai sanar da wanda zai maye gurbinsa marigayi Attahiru ba.

Omokri a shafinsa na Twitter a ranar Litini, 24 ga Mayu, ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya nada wani dan kabilar Ibo don dakatar da karuwar masu neman ballewar kasar daga yankin Kudu maso Gabas.

A cewarsa, ya kamata gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta daina nuna kyama ga iyamirai ta wajen ci gaba ga yankin na gabas.

Sakon Omokri na kamar haka: “Hanya mafi kyawu don yaki da karuwar masu neman ballewa daga yankin Kudu maso Gabas ba ta hanyar bindigogi da harsasai da jiragen yaki masu saukar ungulu ba. Ka ba su ci gaba kuma ka daina nuna son kai. Yi adalci da daidaitawa a yayin nadin ka.

“Ka yi la’akari da wani dan kabilar Ibo don maye gurbin Janar Attahiru. Yi watsi da tunanin wariya da fifiko 97% da 5%. “

Omokri ya kuma nemi shugaban kasan da ya ziyarci kasar Iyamirai, ya rungumi dan takarar shugabancin kasar a zabe ta gaba daga yankin su.

“Ka manta da kiyayyaya da tsoracewar da ka ke wa Iyamirai, Ka ziyarci kowace jihar Igbo (Buhari bai ziyarci kasar Igbo ba tun zaben 2019). Sanya sarakunan Igbo su zama mashahuran shugabannin jami’o’in tarayya a Arewacin Najeriya.

“Da gaske ne a nemi wata ƙasa ta kudu maso gabas a cikin tsarin sake fasalin tsarin mulki, don daidaita da sauran yankuna na siyasa. Karfafa wa babbar jam’iyyar siyasa gwiwa don la’akari da dan takarar Shugabancin Igbo.

“Ka rungumar ‘yan Iyamirai, su ma za su rungumi Najeriya,” Omokri ya rubuta.