Connect with us

Labarai Hausa

Sabuwar Labari: Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 20 A Bauchi

Published

on

Wani sabon barkewar cutar kwalara a jihar Bauchi ya kashe akalla mutane 20 a wasu sassan jihar, Naija News ta ruwaito.

An tattaro da cewa kimanin mutane 322 a halin yanzu ke kame da annobar a Jihar.

Kwamishinan kula lafiya na jihar, Dakta Aliyu Mohammed Maigoro, ya yi bayani kan halin da ake ciki yayin ganawa da manema labarai a safiyar ranar Talata, 25 ga Mayu.

Ya ce barkewar cutar ta bazu a cikin kananan hukumomi tara da ke a jihar. Hakan ya faru ne tun lokacin da aka sanar da bullar cutar a watan Afrilu.

A cewar Kwamishinan, lamarin ya nuna cewa wani mara lafiya ne dan shekaru 37, wanda aka kwantar da shi a babban asibitin Burra a ranar 24 ga Afrilu, 2021.

Karin bayyani zai biyo a nan jin kadan…