Connect with us

Labarai Hausa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Kansa A Ebonyi

Published

on

Wani dan kunar bakin wake, ranar Talata, 25 ga Mayu ya kashe kansa a yayin rigar kunar bakin wake da yake sanye da ita ta fashe a jikinsa.

Lamarin ya faru ne a gaban sananan babban Kasuwar Eke, Afikpo, da ke karamar Hukumar Afikpo ta Arewa a Jihar Ebonyi.

Wata majiya a yankin ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar Talata. A cewar majiyar, “Ya yi kokarin shiga makarantar firamare ta Amaizu / Amangballa amma jami’an tsaron makarantar sun mayar da shi tunda ba zai iya ba da dalilinsa na ziyarar ba.

“Nan take ya fara gudu zuwa cikin wani daji kusa da wurin kafin aka ji babbar kara.”

Majiyar ta ce mazauna garin sun bazama domin kare rayukansu lokacin da bam din ya fashe amma suka sake haduwa a inda abin ya faru ‘yan mintoci kadan bayan da suka gano wanda ake zargin dan kunar bakin waken ya kwanta a cikin jininsa.

Majiyar, wacce ta lura cewa lamarin ya faru ne kusa da Kasuwar Eke da ke Afikpo, wanda ya kasance babbar kasuwa a yankin, ta ce akwai tashin hankali da firgici a cikin al’umma bayan lamarin.

An tattaro cewa bangaren gaban dan kunar bakin waken ya lalace saboda tasirin nauyin bam din.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Zaman Lafiya na kan iyaka, Cif Stanley Okoro-Emegha, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya lura cewa har yanzu bai samu cikakken bayanin abin da ya faru ba.