Connect with us

Labaran Nishadi

Liverpool Ta Bi Sahun Sevilla Ga Neman Sayan Onuachu

Published

on

Majiyoyi sun bayyana da cewa Liverpool ta shiga zawarcin neman sayan dan wasan gaba na Genk, Paul Onuachu.

A cewar Fichajes, Liverpool tana shiga layin yaki da Sevilla da kuma RB Leipzig kan sanya hannu ga sayan dan kwallon Najeriyar a kasuwar musayar ‘yan wasan bazarar nan.

Naija News ta kula da cewa Onuachu a haka yana da gwalagwalai 35 da ya ci, ya kuma taimaka wajen cin kwallaye biyar a wasanni 41 a duk wasannin da ya buga wa Genk a wannan kakar.

Dan wasan mai shekaru 26 ya kuma jawo hankalin Lazio, Celtic, da Lyon a baya. Onuachu a ranar Litinin aka sanya sunansa a kungiyar kwallon kafa ta Belgium ta kakar wasanni.

Tarihin wasa ta nuna da cewa Onuachu ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara ta Jupiler Pro League na kakar 2020/21 da kuma kyautar takalmin zinare.

A halin yanzu, Liverpool na son sake daya daga cikin ‘yan wasan ta, watau Xherdan Shaqiri ko Divock Origi a wannan bazarar.

Idan kuwa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan wasan ya bar Anfield, to sa hannun Onuachu zai iya zama siye ne na hankali don tallafawa Roberto Firmino, Mohamed Salah, Sadio Mane da Diogo Jota, Naija News ta fahimci hakan.