Connect with us

Labaran Nishadi

Luka Modric Ya Tsawaita Kwantiragin Real Madrid Har Zuwa 2022

Published

on

Fitaccen dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric ya sanya hannu kan tsawaita kwantiraginsa wanda zai ci gaba da zama a kulob din har zuwa karshen kakar wasa mai zuwa.

Naija News ta fahimci cewa babban Kattai a gasar La Liga ne ta sanar da zancen a ranar Talata, 25 ga Mayu.

Dan wasan na Croatia din mai shekara 35, wanda ya lashe Ballon d’Or a 2018, ya buga wa Madrid wasanni 391 tun lokacin da ya koma daga Tottenham a 2012.

“Dan wasan dan kasar Crotia zai kasance a kungiyar mu har zuwa 30 ga watan Yuni, 2022,” in ji Real Madrid a cikin wani gajeren bayani.

Wannan kamfanin dilancin labarai ta yanar gizo ta mu ta kula da cewa Modric ya ci gaba da kasancewa babban dan wasa ga ‘yan wasan Zinedine Zidane a wannan kakar, inda ya ci kwallaye shida a wasanni 48.

Yayin yada yawu kan zancen tsayin sa a Madrid, Modric a shafinsa na Twitter ya ce: “Ina farin ciki da alfahari da ci gaba da sanya rigar mafi kyawun kungiyar kwallon kafa a duniya,”

Naija News ta kula da cewa wannan kakar da aka kamala ya kasance lokaci mai matukar wahala ga zakarun Turai din masu nasara 13.

Sun sha kashi a hannun Chelsea a wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai sannan kuma Atletico Madrid ta dauki kofin La Liga a ranar Asabar.