Connect with us

Labarai Hausa

Mutane 2 sun rasa rayukansu a hatsarin gobarar tirela a Bauchi

Published

on

Rahoto da ke isowa ga Naija News a wannan sa’a ya bayyana da cewa akalla mutane biyu ne aka tabbatar da mutuwar su a wani hatsarin gobara wanda ya faru a ranar Litinin.

An ruwaito da cewa mutanen sun mutu lokacin da wata motar tirela ta kama da wuta a Azare, hedikwatar karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.

Kamfanin dilancin labarai ta Daily Post ta ruwaito da cewa mutane da yawa sun samu raunuka daban-daban a hatsarin.

Majiyoyi sun bayyana cewa tirelar ta kama da wuta ne a wata wuri inda ake faka tireloli, a nan kan hanyar Azare-Jama’are, inda direban ya shiga domin aiwatar da wasu gyare-gyare a kan motar da aka bayyana a cikin bita ta welder a ranar Litinin da rana.

An samu labarin cewa hatsarin gobarar ya faru ne yayin da walda ke gyarar tirelar. An ce silinda da wani mai walda yake amfani da shi kan aiki a kan wata mota ta fashe kuma gas din ya bazu zuwa inda ake gyaran tirelar.

Naija News ta gane da cewa fashewar ta haifar da annoba a wajen da ake faka tirelolin, sanadiyar da mutane suka tsere da gudu don tsira da rayukansu sakamakon wutar da ta yadu.

Gobarar wutar an bayyana da cewa ta ci mutuncin mutane da duk wani abu da ke kusa.

Wata majiya ta ce direban tirelar ya yi kokarin fitar da motarsa ​​daga wajen, amma abin takaici sai wutar ta kama da shi kuma ya mutu a cikin yanayin.

Majiyoyi sun bayyana cewa an kai mutane 11 da suka kone sosai a hatsarin zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC), Azare da Babban Asibitin Azare don kula da lafiyarsu.