Connect with us

Labaran Siyasa

Tinubu, Tare Da Wasu Sun Ziyarci Buhari A Aso Rock – [Kalli Hotuna]

Published

on

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a daren ranar Litini, 24 ga Mayu, ya kai ziyarar ta’aziyya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa.

Naija News ta ruwaito da cewa ziyarar Tinubu ta kasance ne game da rasuwar babban hafsan sojojin kasar, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Tawagar da ta ziyarci Buhari a daren Litinin kuma ta hada da Cif Bisi Akande da wasu shugabannin kudu maso yamma.

Da yake bada tabbacin ziyarar, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad ya shiga shafinsa na Twitter a ranar Talata inda ya rubuta: “A daren jiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ziyarar ta’aziyya daga shugabannin Kudu maso Yamma sakamakon mummunan hatsarin jirgin sama da ya faru ranar Juma’a a Kaduna wanda ya yi sanadin rayukan marigayi babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Attahiru, tare da wasu hafsoshin soji 10.”

Naija News ta fahimci cewa ziyarar ta biyo ne bayan ‘yan sa’o’i da Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar daga yankin kudu maso yamma suka bayyana goyon bayansu ga dokar hana kiwon dabbobi a fili.

Shugabannin sun bayyana goyon bayansu ga manufar da gwamnonin kudu suka kafa kan hana kiwo a fili a yankinsu.

Wannan ya na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taro da suka fitar a ranar Lahadi a gidan Marina da ke Legas.

Kalli wasu hotuna daga ziyarar da aka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren Litini a kasa:

Naija News ta ruwaito da cewa taron da manyan shuwagabanan yankin suka yi a Legas ranar Lahadi da ta gabata, ya samu halartar Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila, Cif Bisi Akande, gwamnonin APC na Kudu maso Yamma, da sauran shugabanni.

Baya ga bayyana goyon baya ga dokar hana kiwo a fili, shugabannin sun kuma yi kira da a gudanar da tsarin tarayya na gaskiya a Najeriya ta fuskar samar da albarkatu da iko.

Kodashike dai, fadar shugaban kasa ta yi tir da shirin da Gwamnonin Kudu suka gabatar don aiwatar da dokar hana kiwo a fili. A wata sanarwa a ranar Litinin ta bakin kakakin shugaban, Garba Shehu, fadar shugaban kasar ta ce shirin da gwamnonin suka yi na hana kiwo a fili a Kudancin kasar nan na “halaccin doka ne”.

A cewar fadar shugaban kasar, kudurin da aka cimma a Asaba, babban birnin jihar Delta, ba zai magance rikicin manoma da makiyaya ba.

Shehu ya lura da cewa matakin da gwamnonin suka yi a yayin taron da suka gabata a Asaba, jihar Delta ya saba wa ‘yancin da tsarin mulki ya baiwa ’yan Najeriya na rayuwa da yin kasuwanci a kowane bangare na kasar nan, ba tare da la’akari da irin asalin dan kasa ba.