Connect with us

Labarai Hausa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai Biyar A Wata Hari A Ofishin ‘Yan Sandan Enugu

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san da su ba a sanyin safiyar ranar Talata sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Iwollo da ke karamar hukumar Ezeagu a jihar Enugu inda suka yi kaca-kaca da ofishin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Mista Mohammed Aliyu, a yayin tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ce tuni ya kasance a wajen don tabbatar da irin asarar da aka yi.

“Zamu tura karin bayanai zuwa ga jama’a da zaran mun kammala binciken farko a kan al’amarin” in Aliyu.

Sai dai, wani ganau, wanda ya bukaci kada a ambaci sunansa, ya shaida wa NAN cewa maharan sun far wa bangaren jami’an ne da yawansu da safiyar ranar.

Ya kara da cewa harin ya jefa daukacin al’ummar Iwollo cikin tsoro da firgici cikin dare. “Sun yi nasarar lalata gine-ginen da ke cikin tashar ‘yan sandan,” inji shi ganau.

“’Yan ta’addan akalla sun kashe ‘yan sanda biyar da suka tari gabansu a lokacin harin”.

Ku tuna cewa a ranar 21 ga Afrilu, wasu ‘yan bindiga da ba a san su ba sun harbe wasu jami’an ‘yan sanda biyu har lahira a yayin wani hari da suka kai ofishin ‘yan sanda na Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu.

An kuma kone tashar baki daya da misalin karfe 2:30 na safe.