Connect with us

Labaran Nishadi

‘Yan Sanda Sun Cafke Ahmad Isah, Shugaban Gidan Radiyon Brekete

Published

on

‘Yan Sandan babban birnin tarayya (FCT), sun cafke Ahmad Isah, babban shahararre da kuma shugaban gidan radiyon ‘Brekete’

Naija News ta samun sanin cewa an kama Isah, Babban Jami’in Gidan Rediyon Kare Hakkin Dan Adam na 101.1FM Abuja, saboda cin zarafin wata mata da ake zargi da kunar ‘yar yayanta a kai.

An kama ‘Ordinary President’ kamar yadda ake yawan kiransa, bayan wata mumunar hali da aka nuna a wani shirin bidiyo na BBC Africa Africa Eye.

Matar da Isah ya kyafta wa mari ta rigaya ta furta cewa ta watsa wa diyar dan uwanta da ake zargi da maita kananzir,  da kuma cinna mata wuta a kai.

Naija News ta ruwaito da cewa yayin suka da jita-jita akan matakin Isah da marin matar, shahararren ya nemi afuwa.

Amma dai, a safiyar yau Talata, an bayyana kamun Isah ne a shafin Twitter na kamfanin labarai na Brekete.

“Shugaban shirin Brekete Radio da TV a safiyar yau ya girmama gayyatar zuwa ga rundunar ‘yan sanda ta FCT,”

“Muna son jama’a su sani cewa har yanzu ba mu sa shi ga ido ba sami furci daga bakin sa ba.”

“Na gode da rabawa da kuma sake aikowa,” bayanin a kan Twitter na kamar haka.