Connect with us

Labarai Hausa

‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga Biyu A Imo

Published

on

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo, a ranar Talata, ta sanar da kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar wuta da ta dauki tsawon awanni a yankin Ohaji / Egbema na jihar.

Naija News ta sami sanin cewa jami’an tsaron sun kwato bindiga kirar gida da alburusai daga hannun ‘yan fashin da aka kashe.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Bala Elkana, yayin bada tabbacin yanayin ga manema labarai a Owerri, ya ce ana zargin ‘yan fashin suna daga cikin gungun ‘yan kungiyar da suka kai hari a gidan yarin Owerri da kuma hedkwatar rundunar’ yan sanda a Owerri, a ranar 5 ga Afrilu.

Elkana ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta Imo ta kashe wasu ‘yan ta’addan da suka kitsa harin da aka kai hedkwatar rundunar da kuma cibiyar gidan yari a watan Afrilu, 2021. Sun gano bindiga kirar AK 47 dauke da tarin harsasai.

“Dangane da umarnin da Sufeto Janar na ’Yan sanda, IGP Usman Alkali Baba ya ba Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Imo, CP Abutu Yaro, don tabbatar da cewa an cafke ’yan kungiyar asirin da suka kai hari a hedkwatar rundunar Owerri da kuma Cibiyar Gidan Yari da ke a Owerri, Rundunar a ranar 24th Mayu, 2021, ta gudanar da kyakkyawan zagaye da bincike a Ocha Community, Awara a karamar hukumar Ohaji/Egbema na jihar Imo.

“’Yan ta’addan sun shiga artabu. A yayin musayar bindigar wanda ya dauki kimanin awanni biyu, wasu mutane biyu da ake zargi sun yi niyyar kitsa kai harin a Hedikwatar ‘Yan sanda da Cibiyar Gidan Yarin Owerri a ranar 5 ga Afrilu, 2021, sun ji mummunan rauni.

“Wadanda ake zargin su ne Unchenna Elendu na yankin Umukusu Ocha da Elu Osinachi na Umuobube Awara.

“An kai mutanen biyu da ake zargi zuwa asibiti don duba lafiyarsu. Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar Uchenna a lokacin da ya dawo yayin da Osinachi Elu wanda yake cikin suma, a baya an tabbatar da cewa ya mutu.

”An samu bindiga mai suna Ak47 Rifle mai lamba 11654 da kuma tarin harsasai masu rai. Har ila yau, an kwato wasu tarin harsasai, adduna da layu wadanda aka daure a kugu na wadanda ake zargin.

“Za a ci gaba da gudanar da aikin binciken har sai an hukunta duk wadanda suka aiwatar da mummunan harin,” inji bayanin dan sandan.