Connect with us

Labaran Siyasa

Zargi Ba Laifi Bane, Ya Kan Karfafa Dimokradiyya – Gwamna Sule

Published

on

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya sake nanata da cewa gwamnatinsa tana a bude don karban zargi mai kyau, yana mai cewa irin wannan zargi kan karfafa dimokuradiyya da kyakkyawan shugabanci.

Naija News ta ruwaito da cewa Sule ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin a Karamar Hukumar Keana ta Jihar yayin wata ganawa da jama’a don bikin cikar gwamnatinsa shekaru biyu.

Ya ce mahimmancin rangadin shi ne domin ba shi damar ziyartar kowace karamar hukuma don yi wa mutane godiya, musamman iyayen gidan sarauta da ke ba shi goyon baya a cikin shekaru biyu da suka gabata da kuma neman ƙarin tallafi.

Gwamnan ya ce rangadin mayar da martani wata dama ce a gare shi don haduwa ido-da-ido da mutanen da galibi ke wahalar ganin sa da kan su tunda ya hau mulki a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sule ya kara da cewa gwamnatinsa ta na marabcin suka ko zargi da shawarwari kan inda ta yi ba daidai ba don neman ci gaba.

“Bisa ga taron da aka yi, mutane sun samu damar ganin mu kai tsaye don yaba mana a inda muka yi daidai ko sukar mu a inda muka yi kuskure.”

“Babu wata matsala a ganin mutane sun yi mana suka da tambaya da kuma neman sanin dalilin aikata wata abu, idan babu suka da adawa, babu dimokiradiyya,” in ji shi.

“There is nothing wrong in telling us why did you do that instead of doing this if there is no criticism and opposition, there is no democracy,” he said.